logo

HAUSA

Shugaban Ukraine ya bijirewa dukkan sharrudan da Ukraine ba ta amince da su ba

2022-02-27 17:02:38 CRI

Shugaban Ukraine ya bijirewa dukkan sharrudan da Ukraine ba ta amince da su ba_fororder_0227-1

Manazarci na ofishin shugaban kasar Ukraine, Mikhaylo Podolyak, ya bayyana a jiya cewa, shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ki yarda da dukkan sharrudan da Ukraine ba ta amince da su ba, ya amince da yin shawarwari a dukkan fannoni. Podolyak ya bayyana a shafin internet na ofishin shugaban kasar Ukraine a wannan rana cewa, an kawo karshen dukkan yakin ta hanyar yin shawarwari, kasar Rasha ta san ra’ayin kasar Ukraine kan tsarin yin shawarwari da matsayarta. Tilas ne a yi shawarwari yadda ya kamata da tsara shirin daidaita matsalar dake dacewa da moriyar kasar Ukraine da jama’arta.

Bisa sanarwar da aka bayar a shafin internet na ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha a jiya, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova, ta sanar a ranar 25 ga wata cewa, kasashen kungiyar NATO ba su son yin shawarwari, kana ba su son ci gaba da kiyaye tsaron nahiyar Turai bisa tsarin ka’idoji na adalci da kaucewa raba kan al’ummar kasashen biyu. Kungiyar NATO, tana shirin ci gaba da samar wa kasar Ukraine makamai da na’urori, ciki har da samfuran makamai dake lalata makamai masu linzami, wannan ya bayyana cewa, kasar Amurka da kawancenta ba su nuna sha’awa kan daidaita rikicin kasar Ukraine ba.

Fadar shugaban kasar Amurka ta bayar da sanarwa a jiya cewa, domin tinkarar batun Rasha game da daukar matakan soja da ta yi kan kasar Ukraine, shugabannin kasashen Amurka, da kwamitin kungiyar EU, da Jamus, da Faransa, da Birtaniya, da Italiya, da Kanada, sun tsai da kudurin cewa, za a kori bankin Rasha daga tsarin biyan kudi na SWIFT, da daukar matakan kayyade bankin tsakiya na kasar Rasha.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, ya bayyana a cikin sanarwa a jiya cewa, bisa umurnin da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayar, ya ba da iznin samar da gudummawar manyan makamai ga kasar Ukraine da darajarsu ta kai ta dala miliyan 350 don taimakawa kasar Ukraine wajen tinkarar ayyukan soja da Rasha ta kaddamar mata. (Zainab)