Mace mafi karancin shekaru da ta yi shawagi a fadin duniya
2022-02-26 21:15:57 cri
Matukin jirgin sama mai suna Zara Rutherford mai shekaru 19 da haihuwa, ta kafa tarihi a matsayin mace mafi karancin shekaru da ta yi shawagi a fadin duniya, inda ta taba tuka karamin jirginta da ya sauka a yammacin kasar Belgium, kwanaki 155 bayan tashinta.