logo

HAUSA

Sin zata taimakawa aikin gyaran babban filin wasan kasar Saliyo

2022-02-26 17:12:43 CRI

A ranar Juma’a, an mikawa wani kamfanin gine-gine na kasar Sin aikin gyaran babban filin wasa na kasar Saliyo a hukumance, aikin da ake sa ran farawa a watan Maris, kuma ana fatan kammala shi cikin shekaru biyu.

Da yake jawabi a wajen bikin mika aikin, jakadan kasar Sin dake kasar Saliyo, Hu Zhangliang, ya ce aikin zai kasance a matsayin nuna farin cikin huldar dake tsakanin Sin da Saliyo, wacce ta shafe sama da shekaru 50.

A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Ibrahim Nyelenkeh, ministan wasanni na kasar Saliyo, ya bayyana cewa, wannan aiki ya kara bayyana kyakkyawar hulda ta gaskiya wacce ta jima tana wanzuwa tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, “lokaci yayi da za a bunkasa fannin wasanni. Lokaci yayi da ya kamata Saliyo ta fara karbar bakuncin gasar wasannin kasa da kasa."(Ahmad)