logo

HAUSA

Amurka ta kakabawa Putin takunkumi yayi da Rasha da Ukraine ke nuna alamun tattaunawa

2022-02-26 20:41:36 CRI

Amurka ta kakabawa Putin takunkumi yayi da Rasha da Ukraine ke nuna alamun tattaunawa_fororder_1fab2e7339884588835dc147ba7b1f4b

Kasar Amurka ta sanar a ranar Juma’a cewa, ta kakabawa shugaban Rasha Vladimir Putin takunkumi, sakamakon matakin da Moscow ta dauka na kaddamar da hare-haren soji kan kasar Ukraine, yayin da gwamnatocin kasashen Rashar da Ukraine suke bayyana alamun tattaunawar sulhu da juna.

Sakatariyar yada labaran fadar White House, Jen Psaki, ta fadawa taron manema labarai a ranar Juma’a cewa, “domin mara baya ga matakan da kawayenmu na kasashen Turai suka dauka, Amurka zata bi sahunsu wajen kakabawa shugaba Putin, da ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, da mambobin hukumar tsaron kasar takunkumai.”

Tun da farko a ranar Juma’a, mambobin kungiyar tarayyar Turai da Birtaniya, sun amince da rike dukkan kaddarori mallakin Putin da Lavrov dake kasashen Turai.

Sai dai a martanin da ya mayar, kakakin fadar gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov, yace takunkuman basu da wani alfanu, kasancewar babu koda mutum guda cikin manyan jami’an dake da asusun ajiya a kasar Birtaniya ko kuma wata kasa a duniya.(Ahmad)