logo

HAUSA

Kyauta mai wahala

2022-02-26 22:08:09 CRI

Kyauta mai wahala_fororder_693b-8394243613b8b2c6934444866bc65ad0

Sharhi daga Lubabatu Lei

Nepal kasa ce mai ni’ima da kwanciyar hankali da ke bangaren kudancin tsaunin Himalaya, tsaunin mafi tsawo a duniya.

Sai dai hankali ya tashi a kasar a ‘yan kwanakin da suka gabata, inda al’ummar kasar suka kone tutocin kasar Amurka tare da jefa wa ‘yan sanda duwatsu, tare da yin kiran cewa “Mu ki amincewa da MCC”, a yayin da ‘yan sandan suka tarwatsa su da harsashin roba da barkonon tsohuwa da sauransu.

Me ya faru? Ashe, “kyauta” ce da Amurka ta samar ta haifar da rikicin.

A kwanan baya, gwamnatin kasar Nepal ta gabatar da wata yarjejeniyar gudummawar Amurka ga majalisar dokokin kasar, wato yarjejeniyar Millennium Challenge Corporation, ko MCC a takaice, kuma bisa yarjejeniyar, Amurka za ta samar da gudummawar dala miliyan 500 ga Nepal kyauta, wanda za a yi amfani da shi wajen gina wani layin samar da wuta da ma gyaran hanyoyi a kasar. Sanarwar da ofishin jakadancin kasar Amurka a Nepal ya fitar ta yi nuni da cewa, kudin ya kasance “kyauta daga al’ummar Amurka, wanda zai samar da guraben aiki da ma bunkasa manyan ababen more rayuwa, tare da kyautata rayuwar al’ummar kasar.”

Amma an gindaya sharruda kan wannan “kyauta”, ciki har da batun dake nuna cewa “yarjejeniyar MCC tana sama da dokokin kasar Nepal” “Kotun kasar Nepal ba su da ikon shari’a kan ma’aikatan MCC na Amurka” da sauransu. To, da haka za a gane cewa, da a ce kyauta ne, ya fi dacewa a kira ta yarjejeniya maras adalci. Hakan ya sa an yi ta fama da sabani kan yarjejeniyar a cikin kasar Nepal, don haka har yanzu ba a kai ga aiwatar da ita ba duk da cewa an daddale ta tun a shekarar 2017. Amma ga Amurka ta kasa jira, har ma a kwanan baya, majalisar gudanawar kasar ta yi wa Nepal barazana cewa, dole ne ta yanke shawara kan ko za a duba tare da zartas da yarjejeniyar, in ba haka ba, huldar kasashen biyu za ta fuskanci mummunan tasiri.

Lalle, da barazana ce ake ba kyauta? Kuma wane irin gudummawa ce za ta iya kasancewa tana sama a kan dokokin wata kasa mai mulkin kai?  A zahiri dai, yarjejeniyar ta lalata ikon kasar Nepal na mulkin kai da ma mutumcin al’ummar kasar.  A matsayinta na kasa da ke fuskantar koma bayan ci gaba, babu shakka, Nepal na bukatar gudummawar kasa da kasa, amma tambayar a nan ita ce, ko akwai kasar da za ta yi musanyar gudummawar dala miliyan 500 da mulkin kanta da ma mutumcin al’ummarta?

A hakika, MCC shiri ne da Amurka ta tsara bayan harin “9.11” kan yunkurin shawo kan kasashe masu tasowa. Shirin yana karkashin kamfanin Millennium Challenge Corporation, wanda ke da sunan mai zaman kanta, amma kuma ke karkashin jagorancin gwamnatin Amurka.

MCC yana jawo hankali, amma kuma ba abu ne mai sauki ba a kai ga cika sharudan da Amurka ta gindaya.

Amurka ta kuma ba kyautar ga kasashen Afirka da dama, ciki har da Madagascar da Tanzania da Ghana da Benin da sauransu, sai dai an dakatar da yarjejeniyar a kasashen da dama wadanda “ba su jin maganar Amurkar”.  A shekarar 2009, kamfanin MCC ya dakatar da gudummawar ga Madagascar sakamakon yadda aka mika mulkin kasar “ba ta hanyar dimokuradiyya ba”.  Sai kuma a shekarar 2016, Amurka ta yi barazanar kawo karshen yarjejeniyar bayan da ta ci tura wajen haifar da tasirinta ga babban zaben kasar Tanzania, sai dai shugaban kasar Tanzania a wancan lokaci John Magufuli ya ki yarda da abin da Amurka ke so, matakin da ya sa kamfanin MCC ya janye jarinsa, tare da illata tsarin samar da wutar lantarki da ake ginawa a kasar.

Ta haka muke iya ganin cewa, MCC mataki ne da Amurka ta dauka don shawo kan kasashe masu tasowa ta fannonin siyasa da tattalin arziki da sauransu.  Abin farin ciki shi ne karin kasashe masu tasowa sun fahimci hakan. Bisa ga wani rahoton da ofishin hidimar nazari na majalisar dokokin Amurka ya gabatar, an ce, karin kasashe na nuna rashin amincewa da MCC.

Daidai kamar yadda Madam Hua Chunying, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a kwanan baya cewa, “Ta yaya ake iya ba wani kyauta ta hanyar barazana? Wannan kyauta ce ko akwatin Pandora?”