logo

HAUSA

Kasar Sin na goyon bayan Rasha da ta yi shawarwari da Ukraine don daidaita matsalar da ake fuskanta

2022-02-25 23:51:53 CRI

Kasar Sin na goyon bayan Rasha da ta yi shawarwari da Ukraine don daidaita matsalar da ake fuskanta_fororder_微信图片_20220225234628

A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta yanke shawara kan matsayinta ne bisa la'akari da cancantar batun Ukraine. Ya ce ya kamata a yi watsi da tunanin yakin cacar baka, da ba da muhimmanci, da mutunta halastacciyar kulawar dukkan kasashe a fannin tsaro, da samar da tsarin tsaron Turai mai daidaito, inganci da dorewa, ta hanyar yin shawarwari. Kana kasar Sin tana goyon bayan Rasha, da ta yi shawarwari da Ukraine don warware matsalar. Kaza lika ko da yaushe kasar Sin na daukar matsayin mutunta mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasa na kasashe daban daban, da kiyaye manufofi, da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD. A nasa bangaren, Putin ya ce yana son yin shawarwari tare da Ukraine.

A hakika, zantawa mai matukar muhimmanci ce, wadda ta kasance karin kokarin da kasar Sin ta yi wajen sa kaimin daidaita batun Ukraine a siyasance. Baya ga haka, zantawar ta kuma isar da wani muhimmin sako, wato duk da rikicin soja da ya auku a tsakanin Rasha da Ukraine, amma har yanzu akwai damar daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari.

Lalle, furucin ya bayyana cewa, yin fito-na-fito ba zai kai ga warware matsala ba, kuma yin shawarwari shi ne zabi mai hankali.

A wata sabuwa, sakataren watsa labarai na fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov, ya bayyana cewa, shugaba Putin ya shirya tura tawagar gwamnatin sa zuwa Minsk, domin shiga tattaunawar da za a yi tare da tawagar kasar Ukraine.

Gamayyar kasa da kasa na fatan Rasha da Ukraine su kai zuciya nesa, kuma su daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari.  Ra’ayin kasar Sin kan batun Ukraine, ya yi daidai da matsayinta a kullum, wato a martaba mulkin kai da cikakken yankunan kasa da kasa, kuma a kiyaye tsarin dokokin MDD, kuma za ta ci gaba da kokarinta na ingiza yin shawarwari a tsakanin masu ruwa da tsaki, ta yadda za a kai ga warware batun Ukraine a siyasance.(Lubabatu)