logo

HAUSA

An samu tsoffin ’yan sandan Amurka da hannu na keta hakkin George Floyd

2022-02-25 09:42:30 CRI

An samu tsoffin ’yan sandan Amurka da hannu na keta hakkin George Floyd_fororder_0225-Ahmad-Floyd

Mai shara’a a Amurka ya tabbatar da samun tsoffin jami’an ’yan sandan birnin Minneapolis uku da laifin take hakkokin George Floyd, wato Ba’amurke bakar fata, wanda kisan gillar da aka yi masa a watan Mayun shekarar 2020, ya haifar da barkewar zazzafar zanga-zanga a fadin kasar.

Tou Thao, mai shekaru 36; da J. Alexander Kueng, mai shekaru 28; da kuma Thomas Lane, mai shekaru 38, an yanke musu hukunci a ranar Alhamis, bayan shafa tsawon wata guda ana gudanar da shara’ar a kotun Saint Paul, dake birnin Minneapolis, sakamakon yadda suka yi biris da gangan game da bukatar duba lafiyar Floyd.

Thao da Kueng, ana kuma tuhumarsu da gaza kai dauki domin dakatar da amfani da karfin da tsohon jami’in dan sanda Derek Chauvin ya yi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Floyd. (Ahmad)