logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki cikin batun Ukraine suka kai zuciya nesa

2022-02-24 10:26:58 CRI

Kasar Sin ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki cikin batun Ukraine suka kai zuciya nesa_fororder_220224-Fa'iza-matsayin Sin kan batun Ukraine

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga dukkan bangarorin dake da ruwa da tsaki cikin batun Ukraine, su kai zuciya nesa.

Zhang Jun, ya shaidawa wani taro game da Ukraine da babban zauren MDD karo na 76 ya gudanar cewa, kasar Sin na mayar da hankali kan yadda batun na Ukraine ke wakana. Kuma matsayar kasar game da kare cikakken ’yanci da yankunan dukkan kasashe, ba ta sauya ba. Yana mai cewa, ya kamata a hada hannu wajen kiyayewa da daukaka ka’idojin MDD.

A cewarsa, kasar Sin na kira ga dukkan bangarori su amince da muhimmancin aiwatar da ka’idar tsaro a dunkule da ci gaba da tattaunawa da tuntuba, da lalubo mafita domin magance damuwar juna ta hanyoyin zaman lafiya, kuma bisa daidaito da mutunta juna. Ya kara da cewa, Sin na maraba tare da karfafa gwiwar samar da duk wani yunkuri dake da nufin samar da mafita ta hanyar diflomasiyya cikin sauki. (Fa’iza Mustapha)