logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren ababen more rayuwa a matsayin wanda zai bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar

2022-02-24 10:20:00 CRI

Hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren ababen more rayuwa a matsayin wanda zai bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar_fororder_220224-Fa'iza-China-Africa cooperation

Wata kwararriya kan harkokin cinikayya da tattalin arziki ta kasar Ghana, Abena Oduro, ta ce hadin gwiwa tsakanin nahiyar Afrika da kasar Sin a fannin ababen more rayuwa, za ta bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar Afrika.

Abena Oduro, malama a sashen nazarin tattalin arziki na Jami’ar Ghana, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, raya ababen more rayuwa da suka shafi cinikayya, zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin ’yanci ta nahiyar Afrika.

Ta ce ababen more rayuwa da ake bukata cikin gaggawa sun hada da layukan dogo da tituna da hanyoyin jiragen sama, wadanda babu isassun da za su saukaka jigilar kayayyaki da hidimomi tsakanin wurare daban-daban, kamar yadda yarjejeniyar ciniki cikin ’yancin ke hasashe. (Fa’iza Mustapha)