logo

HAUSA

Kasashen gabashin Afrika za su gudanar da atisayen soji a Uganda

2022-02-24 09:59:09 CRI

Rundunar sojin Uganda, ta ce sama da sojoji 1,500 daga kasashen kungiyar raya gabashin Afrika EAC ne za su gudanar da atisayen soji a Uganda.

Rundunar ta bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, fararen hula za su hadu da dakaru daga kasashen Uganda da Tanzania da Kenya da Rwanda da Burundi da Sudan ta Kudu, yayin atisayen soji na kungiyar EAC karo na 12.

A cewar sanarwar, an tsara cewa, shirin wanda zai gudana a watannin Mayu da Yuni a gabashin Uganda, zai nazarci kwarewar dakarun wajen tunkarar kalubalen tsaro masu sarkakiya.

Yayin wani taro da aka gudanar dangane da shirya atisayen a jiya Laraba, Col Rapheal Kiptoo, wanda ya wakilci Sakatare Janar na kungiyar EAC, ya ce atisayen zai kara inganta dunkulewa da aiki cikin hadin gwiwa, tsakanin dakarun yankin. (Fa’iza Mustapha)