logo

HAUSA

MDD ta yi tir da tsaren jami’anta na wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

2022-02-24 10:05:49 CRI

MDD ta yi tir da tsaren jami’anta na wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya_fororder_220224-Fa'iza-CAR

Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya yi suka da kausasan kalamai, kan tsare jami’ai 4 na shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wato (MINUSCA), yana mai kira da a sake su nan take.

A ranar Litinin ne jami’an tsaron kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya suka tsare jami’an a birnin Bangui, yayin da suke yi wa wani babban jami’in shirin na (MINUSCA) rakiya.

Sakatare Janar din ya jadadda cewa, bisa yarjejeniyar girke sojoji dake tsakanin MDD da gwamnatin kasar, dangane da shirin wanzar da zaman lafiya na MINUSCA, wadannan jami’ai suna da hakkoki na musamman da ma rigar kariya saboda MDD.

Antonio Guterres ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, ta kiyaye dukkan tanade-tanaden dake kunshi cikin dokokin kasa da kasa, ciki har da yarjejeniyar girke sojojin, ta kuma saki wadannan jami’ai nan take ba tare da wani sharadi ba. (Fa’iza Mustapha)