logo

HAUSA

Jakadan Sin A Nijer Ya Gana Da Ministan Aikin Gona Na Kasar Nijer

2022-02-23 14:49:10 CRI

Jakadan Sin A Nijer Ya Gana Da Ministan Aikin Gona Na Kasar Nijer_fororder_0223-01

A jiya ne, jakadan Sin dake kasar Nijer, Jiang Feng ya gana da ministan aikin gona na kasar Nijer Alambedji Abba Issa, inda suka yi musayar ra’ayoyi a fannonin dangantakar dake tsakanin Sin da Nijer, da hadin gwiwar aikin gona a tsakaninsu da sauransu.

Jakada Jiang ya bayyana cewa, Sin da Nijer suna sada zumunta da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu, a fannoni daban daban a shekarun baya baya nan. Hadin gwiwar aikin gona wani muhimmin bangare ne na aikin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Niger. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manyan ayyuka 9 da Sin da kasashen Afirka suka aiwatar a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, cikin har da aikin yaki da talauci, da samar da moriya ga manoma. Sin tana son yin amfani da wannan dama don kara yin hadin gwiwa tare da kasar Nijer a fannin aikin gona don amfanawa jama’ar kasashen biyu.

A nasa bangaren, minista Alambedji Abba Issa ya nuna yabo ga hadin gwiwar sada zumunta a tsakanin Nijer da Sin, kana ya nuna godiya ga kasar Sin, bisa kokarinta wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin ta jawo hankalin kasa da kasa sosai, tana da fasahohi game da samar da hatsi da zamanintar da aikin noma da sauransu. Kasar Nijer tana son koyi da fasahohin kasar Sin, don sa kaimi ga raya hadin gwiwar aikin noma a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)