logo

HAUSA

Sin na zage damtse wajen samar da isasshen hatsi da kaucewa sake tsunduma kangin talauci

2022-02-23 20:03:04 CRI

Sin na zage damtse wajen samar da isasshen hatsi da kaucewa sake tsunduma kangin talauci_fororder_VCG11426166508

Gwamnatin kasar Sin, ta fitar da kundi na daya na shekarar 2022, wanda ya fayyace dukkanin ayyukan da za a gudanar wajen ingiza raya yankunan karkara, da tabbatar da samar da isasshen abinci, da kuma tabbatar da ganin wadanda suka fita daga talauci basu sake afkawa cikin kangin talauci ba.

Kundin na shekara shekara, wanda a bana aka fitar a jiya Talata, ya kan yi nuni ga muhimman ayyukan da kasar ta sanya gaba. Tun daga shekarar 2004, wato shekaru 19 zuwa yanzu, fannin noma da raya karkara ne ke kasancewa a sahun farko, cikin ayyukan da kundin ke gabatarwa.

Kundin ya yi kira da a aiwatar da matakan samar da daidaito, da fadada samar da albarkatun gona, da bin dabarun yalwata kudaden shigar manoma.

Yayin taron manema labarai da aka kira a Larabar nan, ministan ma’aikatar gona da raya karkara na Sin Tang Renjian, ya ce burin Sin shi ne tabbatar da daidaito a adadin hatsi da kasar ke samarwa, ta yadda a duk shekara, yawan yabanyar hatsi a kasar zai kai sama da tan biliyan 650.

A nasa bangare, mataimakin daraktan babbar tawagar jami’an raya karkara na kasar Wu Hongyao, ya ce domin kiyaye ci gaba da aka samu a fannin rage talauci, mahukuntan Sin za su kara azama, wajen bunkasa masana’antu, wadanda za su yaukaka kudaden shigar iyalai mazauna karkara. (Saminu)