logo

HAUSA

Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing ta zarce sa’a

2022-02-23 09:13:30 CRI

Bayan kammala gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing da aka kammala a ranar 20 ga watan nan na Fabarairu, masharhanta da dama sun bayyana gasar da cewa ta zarce sa’a, idan an duba wasu muhimman sauye sauye da ci gaba da aka gani, yayin wannan gasa ta shekarar 2022.

Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing ta zarce sa’a_fororder_220223世界22008-hoto1

Bayan kammalar gasar ta bana, kasashen dake sahun gaba wajen lashe lambobin yabo sun hada da Norway mai lambobin Zinari 16 da Azurfa 8 da Tagulla 13, ta kuma hada jumillar lambobi 37. Sai kuma Jamus mai lambobin Zinari 12 da Azurfa 10 da Tagulla 5, ta kuma hada jumillar lambobi 27. Ita ma kasar Sin mai masaukin bakin gasar ta kammala da lambobin Zinari 9 da Azurfa 4 da Tagulla 2, ta kuma hada jumillar lambobi 15. Amurka ce ta 4 da Zinari 8 da Azurfa 10 da Tagulla 7, inda ta hada jumillar lambobi 25. A mataki na 5 kuwa, Sweeden ta samu Zinari 8 da Azurfa 5 da Tagulla 5, ta kuma hada jumillar lambobi 18.

Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing ta zarce sa’a_fororder_220223世界22008-hoto2

Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing, ta gudana cikin tsauraran matakan dakile yaduwar annobar COVID-19. An kuma yi amfani da fasahohin zamani irin su 4k da 8k wajen watsa shirye shiryen gasar, tare da kyamarori na zamani masu saurin tattara hotuna, da bidiyo masu matukar inganci.

A fannin makamashi, kasar Sin ta yi amfani da nau’oin makamashi da ake iya sabuntawa a fileyen wasanni, da kyauyen wasanni da sauran su, domin kare muhalli da ingancin iska, wanda hakan mataki ne da ya yi matukar  burge kowa.

Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing ta zarce sa’a_fororder_220223世界22008-hoto3

Kaza lika gasar ta samu masu kallo daga dukkanin sassan duniya, da adadi mafiya yawa a tarin makamantan ta da suka gabata a baya.

Ko shakka babu gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing da aka kammala, ta aike da wani sako ga duniya, wato bil adama zai ci gaba da hadin gwiwa, tare da raya zumunci, da abota, yayin da ake fuskantar duk wani kalubale da  ka iya fuskantar duniya. (Saminu Hassan, Ahmad Fagam, Sanusi Chen)