logo

HAUSA

Layin jirgin kasan da Sin ta gina na Habasha zuwa Djibouti ya bunkasa ci gaban shiyyar

2022-02-23 10:12:58 CRI

Layin jirgin kasan da Sin ta gina na Habasha zuwa Djibouti ya bunkasa ci gaban shiyyar_fororder_2202236-A1-Habasha

Aikin layin jirgin kasan da kasar Sin ta gina tsakanin birnin Addis Ababa zuwa Djibouti, ya cimma nasarar bunkasa cigaban shiyyar tare da samar da makoma mai kyau.

A cewar ministan sufurin Habasha, Dagmawit Moges, layin dogon mai nisan kilomita 752, wanda ya kasance aikin da aka gudanar karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya shaida cikar burin kasashen Afrika wajen cimma nasarar yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta nahiyar, inda ya zanto muhimmin aikin more rayuwa da ya hade yankunan Afrika.

Ita ma karamar ministar kudin Habasha, Semereta Sewasew, ta jaddada muhimmancin rawar da kasar Sin ke takawa wajen tallafawa muradun ci gaban kasashen Afrika bisa ga tsarin moriyar juna.

Zhao Zhiyuan, jakadan kasar Sin a Habasha ya jaddada kalaman da Moges ya gabatar, inda ya bayyana cewa, layin jirgin kasan na Addis Ababa-Djibouti gagarumin taimako ne wanda ya shafi cigaban dukkan yankunan kasar Habasha da kewaye.

Game da karuwar adadin kasashen Afrika dake kulla yarjejeniya da kasar Sin karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasashe da dama sun samu sabbin tashoshin ruwa na cikin tsakiyar teku, sannan an gina dubban kilomita na titunan mota, da layin jirgin kasa, wadanda suka taimaka wajen kawo sauye-sauye ga ayyukan jigilar kayayyaki a dukkan sassan Afrika, suna daga cikin ayyukan da suka bunkasa ci gaban nahiyar. (Ahmad Fagam)