logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya murnar kaddamar da makarantar Julius Nyerere leadership dake Tanzaniya

2022-02-23 20:50:46 CRI

Xi Jinping ya taya murnar kaddamar da makarantar Julius Nyerere leadership dake Tanzaniya_fororder_AA

Yau laraba ne aka gudanar da bikin kaddamar da makarantar Julius Nyerere leadership dake kasar Tanzaniya, inda babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna.

Xi ya jaddada cewa, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye a halin yanzu, kuma Sin da nahiyar Afirka na kara bukatar zama tsintsiya madaurinki daya fiye da kowane lokaci da ya gabata, da tinkarar kalubaloli, da samar da ci gaba da alheri ga al’umma. Ya ce jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, tana son yin amfani da wannan dama, don inganta mu’amala tare da jam’iyyun siyasar kasashen Afirka daban-daban, da marawa juna baya, wajen neman samar da ci gaba bisa halin da ake ciki a kasashe daban-daban, da zurfafa hadin-gwiwa, da kyautata raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya, a wani kokari na kara bayar da gudummawa, ta raya duniya mai kyau. (Murtala Zhang)