logo

HAUSA

Zargin da aka yiwa matsayin kasar Sin kan batun Ukraine makarkashiya ce

2022-02-23 19:14:03 CRI

Zargin da aka yiwa matsayin kasar Sin kan batun Ukraine makarkashiya ce_fororder_11

Kafafen yada labaran Amurka sun ruwaito cewa, matsayin kasar Sin kan batun kasar Ukraine, ya sabawa manufofin ta na yau da kullum, wato mutunta cikakken ‘yanci da yankin kowace kasa. Game da wannan zargin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Laraba cewa, zargin makarkashiya ce da aka kulla, ko kuma yunkuri ne na jirkita gaskiya.

Madam Hua ta yi nuni da cewa, ra’ayin kasar Sin kan batun Ukraine, ya yi daidai da matsayinta a kullum, wato daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari. Kasar Sin tana tsayawa haikan, kan tabbatar da adalci da zaman lafiya, da yin kira ga kasa da kasa, su lalubo bakin zaren daidaita rikicin duniya bisa ka’dioji, gami da manufofin kundin tsarin mulkin MDD.

A wani labarin na daban kuma, Madam Hua ta zargi wasu ‘yan siyasar yankin Taiwan na kasar Sin, da kwatanta batun Ukraine da batun Taiwan, inda a cewarta, Taiwan ba Ukraine ba ce, kana, yin amfani da batun Ukraine don rura wutar rikici da wasu ‘yan siyasar Taiwan suke yi, rashin tunani ne.

Hua ta yi karin haske da cewa, batun Taiwan ya samo asali ne daga yakin basasar da aka yi wasu shekaru da suka wuce, al’amarin da ya janyo rikicin siyasa tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan. Amma ba’a taba ware Taiwan daga cikin kasar Sin ba, kuma hakan ba zai faru ba, wannan shi ne gaskiyar lamari. (Murtala Zhang)