logo

HAUSA

Najeriya na kokarin zurfafa hanyoyin tattalin arzikin zamani

2022-02-23 10:50:54 CRI

Najeriya na kokarin zurfafa hanyoyin tattalin arzikin zamani_fororder_220223-A3-Nigeria

Wani babban jami’i a Najeriya ya ce, gwamnatin kasar ta bullo da manyan kudurori 17 da nufin zurfafa matakan raya tattalin arzikin zamani na kasar.

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani na kasar, Isa Ali Pantami, ya bayyana hakan a wajen wani taro da masu ruwa da tsaki a fannin kirkire-kirkiren zamani.

Ya ce, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da daftarin kudurorin da aka tsara, wadanda za a gabatarwa majalisar dokokin kasar domin neman amincewarta.

Pantami ya ce, a shirye suke su gabatar da kwararan hujjojin da za su gamsar da majalisar dokokin kasar domin ta amince da kudurorin don mayar da su doka.

Ya kara da cewa, kudurorin wasu muhimman matakan ne da za su tabbatar da cimma nasarar bunkasa tattalin arzikin zamani na kasar.

Ministan ya jaddada aniyar gwamnatin Najeriyar na samar da muhalli mai kyau da tallafin kudade ga masu sha’awar kafa harkokin tattalin arzikin zamani domin su samu damar gudanar da al’amurran cikin nasara a kasar. (Ahmad)