logo

HAUSA

Karin mutane 50 sun kamu da COVID-19 a Najeriya

2022-02-22 10:54:50 CMG

Hukumar dakile yaduwar cututuka ta kasar Najeriya NCDC, ta ce an samu karin mutane 50 da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar, a ranar Lahadi 20 ga wata.

An samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar ne a jihohi daban daban, inda a jihar Imo akwai mutane 22, jihar Lagos na da mutane 14, jihar Rivers wasu mutum 7, a yankin FCT mutane 5, yayin da sauran mutum 2 sun kamu a jihar Delta.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan labari, an gudanar da bincike kan mutane 4,233,363 a kasar Najeriya. Cikinsu an samu mutane 254,293 da suka harbu da cutar COVID-19. An warkar da wasu 230,775, yayin da wasu 3,142 sun rasu sakamakon annobar. (Bello Wang)

Bello