logo

HAUSA

Bunkasa harshen uwa wata dama ce ta samun ci gaba da hadin kan al’umma

2022-02-22 17:52:24 cri

Bunkasa harshen uwa wata dama ce ta samun ci gaba da hadin kan al’umma_fororder_2

Harshe ko yare, wata alama ce ta mutane daban-daban dake akwai a duniya. Shi ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta ware wata rana guda, ta 21 ga watan Fabrerun kowacce shekara, a matsayin ta tunawa da muhimmancin harshen uwa ga ci gaban duniya da al’adu da cudanya tsakanin al’ummun daban daban.

Ban da haka, a ganina, karewa da kyautata amfani da harshen asali na wata kasa ko al’umma, na bada gagarumar taimako ga ci gaban al’umman. Misali, amfani da harshen uwa wajen koyarwa da  gudanar da harkokin kasa, ba karamin taimakawa kasashe masu tasowa zai yi ba wajen rainon al’umma da ciyar da su gaba. Nazarce-nazarce ma sun nuna cewa, dalibai sun fi fahimtar koyarwa cikin harshensu na asali maimakon harshen aro. A yanzu, musammam a kasashe masu tasowa, an fi mayar da hankali wajen koyon harsunan kasashen yammacin duniya musammam harshen Ingilishi maimakon harshen asali na yanki ko al’umma.

Zamana a kasar Sin, ya kara fahimtar da ni irin dimbin ci gaban da kasar ta samu, ba zai rasa nasaba da amfani da harshen Sinanci wajen gudanar da harkokin kasa da koyarwa da duk wani abu da ya shafi al’umma ba. Haka kuma, ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo hadin kai a tsakanin al’ummarta. Duk da cewa akwai tarin kabilu daban-daban a kasar Sin, harshen Sinanci, shi ne harshen da daukacin al’ummar kasar ke amfani da  ita a hukumance.

A tunanina, wannnan kadai misali ne da ya kamata a ce kasashenmu na Afrika sun yi koyi da shi, idan suna son samun ci gaba. Koyon wasu harsunan, shi ma abu ne mai muhimmanci, amma kuma bai kamata garin yin hakan, a manta da harshen asali ba. Ban da haka, koyarwar cikin harshen uwa zai rage kudin da ake kashewa wajen samar da ilimi, haka kuma zai tabbatar da daidaito a wannan fannin, tsakanin yaran da suka fito daga iyalai masu hali da wadanda ba su da hali.

Idan muka yi duba kan manyan kasashen duniya, dukkansu na amfani ne da harsunansu na asali a matsayin babban harshen kasa, amma galibin kasashe masu tasowa, na amfani ne da harsunan kasashen da suka raine su.

A gaskiya, akwai bukatar gwamnatoci su yi duba a kan wannan bangaren a matsayin wata hanya ta neman ci gaban al’umma da hadin kai da uwa uba tabbatar da ilimin zuri’a masu tasowa. Kamar yadda na ce, mayar da hankali kan harshen uwa bai zama watsi da sauran manyan harsunan kasashen waje ba. Sai dai, kamata ya yi harshen uwa ya zama a kan gaba. Kamar a kasar Sin, sai da kowanne dan kasa ya iya harshen Sinanci kafin koyon wasu harsunan waje. Duk inda ka je a duniya, za ka tarar Basine ya iya harshensa kuma zai iya mu’amala da kowanne Basine daga kowanne bangare na kasar Sin. Wannan ma na daya daga cikin dalilan da suka sanya kasar ke kiyaye dadaddun al’adunta na gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni, haka kuma yara da manya duk sun san tarihin wadannan al’adu. (Faeza Mustapha)