logo

HAUSA

Sin da Masar sun samar da alluran rigakafi ga yankin Gaza

2022-02-22 14:13:49 CMG

Sin da Masar sun samar da alluran rigakafi ga yankin Gaza_fororder_220222-Bello-allura

Kasashen Sin da Masar sun yanke shawarar samar da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19, kimanin dubu 500, karkashin hadin gwiwarsu ga Falasdinawan dake zama a yankin Gaza. A ranar Lahadin da ta gabata, an kaddamar da aikin jigilar alluran a birnin Alkahira na kasar Masar.

A wajen bikin fara aikin, jakadan Sin a kasar Masar, Liao Liqiang ya ce, gwamnatocin Sin da Masar sun yi kokarin hadin kai da juna, inda suka dauki wannan mataki don taimakawa al’ummar yankin Gaza wajen dakile annobar COVID-19, da daidaita yanayin ayyukan jin kai. Ta haka an nuna yadda kasashen 2 suke dora muhimmanci kan lafiyar jikin mutanen Falasdinu, da yadda za a iya daidaita al’amuran wurin. Haka zalika, wannan batun ya shaida kyakkyawar huldar hadin kai da ake samu tsakanin Sin da Masar, wadda ta shafi manyan tsare-tsare na dukkan fannoni.

A nasa bangare, Khaled Ghaffar, mukadashin minista mai kula da aikin lafiya da al’umma na kasar Masar, ya nuna yabo kan hadin gwiwar kasashen Masar da Sin a fannin tinkarar annoba, inda ya ce, huldar ta zama abin koyi ga ragowar kasashe.

Madam Nidaa Al-Barghouthy ita ce wakiliyar Falasdinu a kasar Masar, ta halarci bikin kaddamar da aikin samar da tallafin alluran rigakafin ga Falasdinawa, inda ta yabawa kasashen Sin da Masar bisa goyon bayan da suke baiwa al’ummar Falasdinu. Ta ce,

“Yadda kasar Sin da kasar Masar suka samar da tallafin alluran rigakafin cutar COVID-19 ga mutanen Falasdinu dake yankin Gaza yana da muhimmiyar ma’ana, a fannin taimakawa dakile annobar a Falasdinu. A madadin shugabanmu, da gwamnatinmu, da jama’ar Falasdinu, ina matukar gode muku.”  (Bello Wang)

Bello