logo

HAUSA

Ana bukatar yin shawarwari maimakon rura wutar rikici idan ana son daidaita rikicin Ukraine

2022-02-22 20:43:57 CRI

Ana bukatar yin shawarwari maimakon rura wutar rikici idan ana son daidaita rikicin Ukraine_fororder_111

Halin da ake ciki a kasar Ukraine, ya samu babban sauyi a jiya Litinin, inda kasar Rasha ta sanar da amincewarta ga ‘yancin kan “Jamhuriyar Lugansk (LPR)" da “Jamhuriyar Donetsk (DPR)", a matsayin kasashe masu cin gashin kansu dake gabashin Ukraine, matakin da ya jawo kakaba takunkumin kudi daga kasar Amurka, da sauran wasu kasashen yammacin duniya ga Rasha.

A yayin taron gaggawa da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kira dangane da batun Ukraine, kasar Sin ta yi kira ga bangarorin masu ruwa da tsaki da su nuna hakuri, da kaucewa daukar duk wani matakin da zai iya rura wutar rikici.

Akwai dalilai da dama, da suka jawo tabarbarewar halin da ake ciki a Ukraine. Ita dai Amurka ta zama mai hura wutar rikicin. Kwanan nan, Amurka ta rika tallata labaran da suke bayyana cewa, wai Rasha za ta mamaye Ukraine, a wani kokari na sake dawowa da goyon-bayan al’ummar kasar ga gwamnatin Biden, da taka birki ga ci gaban Turai da sauransu.

Amma idan ana son lalibo bakin zaren daidaita rikicin Ukraine, ya dace a zauna a yi shawarwari, maimakon rura wutar rikici. A matsayinta na zaunanniyar kasa dake kwamitin tsaron MDD, matsayin kasar Sin kan batun Ukraine bai sauya ba, wato ya kamata a mutunta kulawar duk wata kasa, da kiyaye ka’idoji gami da manufofin kundin tsarin mulkin MDD.

Ya dace bangarori masu ruwa da tsaki, su nuna hakuri, don hana ta’azzarar halin da ake ciki a Ukraine. Ya kamata kasar Amurka da sauran wasu kasashe su taimaka ga yin shawarwari, maimakon tada zaune-tsaye. Ya dace manyan kasashe su zama kyawawan misalai, na gina duniya mai kyau.  (Murtala Zhang)