logo

HAUSA

Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 34 a Kamaru

2022-02-22 10:30:46 CRI

Cutar kwalara ta yi ajalin mutane 34 a Kamaru_fororder_220222-Ahmad-Kamaru

A kalla mutane 34 ne aka tabbatar da mutuwarsu ya zuwa yanzu, sakamakon barkewar annobar kwalara wacce ta mamaye yankunan jamhuriyar Kamaru, ofishin shirin jinkai na MDD, OCHA, ya bayyana hakan a jiya Litinin.

A kalla shiyyoyi hudu na kasar annobar ta fi yiwa mummunan barna, wanda ya hada har da shiyyar Littoral, inda a can ne babban birnin kasuwancin kasar Douala yake.

Hukumar OCHA ta sanar cewa, a shiyyar kudu maso yamma, mutane 28 ne suka mutu, yayin da wasu 1,055 suka kamu da cutar. Sannan an samu mutane 77 sun kamu tare da mutuwar mutane hudu a shiyyar Littoral, yayin da shiyyar kudancin kasar cutar ta kama mutane 52 tare da kashe mutum biyu, kana a yankin arewa mai nisa an samu rahoton mutane takwas sun harbu da cutar.

An samu rahoton farko na barkewar cutar kwalarar ne a wasu yankunan dake shiyyar Littoral, da kuma shiyyar kudu maso yammacin kasar, a farkon watan Janairu.

A makon jiya, ministan kula da lafiyar al’umma na Kamaru, Malachie Manaouda, ya umarci al’umma da su kasance masu kula da yanayin tsafta, kana su sanar da rahoton alamun kamuwa da cutar ga asibitocin kasar. (Ahmad)