logo

HAUSA

An rufe Beijing Olympic 2022: Shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu?

2022-02-22 15:57:50 cri

An rufe Beijing Olympic 2022: Shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu?_fororder_1

Bayan shafe sama da makwanni biyu ana fafatawa a gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta kasa da kasa karo na 24 wanda Beijing ta karbi bakuncinta a shekarar 2022, zamu iya cewa, da alama kwalliya ta biya kudin sabulu. An dai bude gasar wasannin motsa jikin ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 ne a ranar 4 ga watan Fabrairu, a wani kasaitaccen biki wanda ya samu halartar shugabannin kasashen duniya da dama da manyan shugabannnin hukumomin kasa da kasa. Da yammacin ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu, an gudanar da bikin rufe gasar. Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic ta kasa da kasa IOC, Thomas Bach, ya bayyana rufe gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin rufe gasar, Bach ya bayyana gasar wasannin ta Beijing Olympic 2022 da cewa, “ta musamman ne." Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach sun halarci bikin rufe gasar. Gasar ta Bejing Olmpic 2022 ta samu mahalarta kusan dubu 3 daga kasashen duniya da shiyyo kusan 100. Dama dai tun gabanin fara wasannin, shugabanni da dama sun yi gargadin cewa gasar Olympic gasa ce ta duk duniya kuma bai kamata a nemi siyasantar da ita ba. Tun dai a jajiberin rufe gasar yayin cikakken zama na 139 wanda kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa IOC ya shirya a Beijing, shugaban kwamitin Thomas Bach, ya karrama al’ummar kasar Sin da kofin Olympics, da nufin gode musu saboda goyon-bayansu ga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta bana. Bach ya ce, ba don goyon-bayan mutanen Sin ba, da ba za’a iya shirya gasar bana tare da samun cikakkiyar nasara ba. Duk da cewa an shirya gasar ta bana a cikin wani yanayi na kulle don hana yaduwar cutar COVID-19, amma Bach ya ji dadin cikakken goyon-baya daga al’ummar kasar Sin. Dama dai masu hikimar magana na cewa, “Fata na gari lamirin.” Ko shakka babu, gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 ta isar da wani muhimmin sako ga duniya musamman na neman zaman lafiya, da hadin kan duniya, da sada zumunci, da kawar da kiyayya a tsakanin alummun kasa da kasa, da neman karfafawa juna gwiwa domin cimma nasarar samar da makoma mai kyau ga dukkan bil adama domin a gudu tare a tsira tare.(Ahmad Fagam)