logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bukaci a mayarwa kasarsa kayan tarihinta da aka boye a ketare

2022-02-22 15:07:40 CRI

Shugaban Najeriya ya bukaci a mayarwa kasarsa kayan tarihinta da aka boye a ketare_fororder_220222-Ahmad-Nigeria

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga kasashen duniya, da cibiyoyin kasa da kasa, da hukumomi masu zaman kansu, da kuma hukumomin gwamnati, da su mayarwa kasar kayayyakin fasaharta da aka sace daga kasar aka boye a kasashen waje.

Kiran da shugaba Buharin ya yi na zuwa ne, biyo bayan mayar wa masarautar Benin kayan tarihi na tagulla biyu wanda dakarun sojojin Birtaniya suka sace.

Wadannan kayan fasaha na daga cikin kayan tarihi mafi muhimmanci na Afrika da aka gaje su, wadanda Turawa ’yan mulkin mallaka da masu binciken suka sace suka kai su zuwa Turai daga wata babbar masarautar dake birnin Benin, a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta yi iyakar kokarinta wajen kokarin ganin an maido da kayan fasahar kasar ta Najeriya, inda ya bukaci sauran kasashe da su yi koyi da irin matakin da cibiyoyin suka dauka a baya bayan nan inda suka mayar da tagullar ta Benin. (Ahmad)