logo

HAUSA

MDD ta bukaci tallafin jinkan gaggawa a Somali sakamakon annobar fari

2022-02-22 10:20:33 CRI

MDD ta bukaci tallafin jinkan gaggawa a Somali sakamakon annobar fari_fororder_220222-Ahmad-Somaliya

Hukumar samar da tallafi mafi girma ta MDD dake kasar Somaliya, ta yi kiran a samar da taimakon gaggawa ga al’ummomin kasar Somaliya wadanda bala’in fari ya shafa a yankin Somaliland dake shiyyar arewacin kasar.

Adam Abdelmoula, jami’in shirin ayyukan jin kai na MDD a kasar  Somalia, wanda ya ziyarci yankin Somaliland domin tantance yanayin farin da ake fama da shi ya bayyana cewa, an samu karuwar adadin iyalan da suka kauracewa muhallansu, wadanda suka baro yankunan da farin ya yi wa mummunar barna, inda suke neman mafaka a yankin Somaliland.

Abdelmoula ya bayyana cikin wata sanarwa da aka fitar a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya cewa, wannan lamari yana kara girman matsalar karancin albarkatun da ake da su a yankunan kasar. (Ahmad)