logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci wasu kamfanonin Amurka

2022-02-21 20:51:19 CRI

Sin ta kalubalanci wasu kamfanonin Amurka_fororder_4d086e061d950a7b0e3cd963822589d0f3d3c90e

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta kalubalanci kamfanonin Raytheon da Lockheed Martin na Amurka, saboda hannu da suke da shi a sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai, matakin dake da illa ta fuskar ‘yancin mulki kai da tsaron kasar Sin.

Wang Wenbin ya ce Sin ta sake jaddada kira ga gwamnatin Amurka, da sauran sassa masu ruwa da tsaki da su martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, da yarjejeniyoyin da sassan biyu suka sanyawa hannu, kana ta dakatar da sayarwa yankin Taiwan makamai, da ma kulla duk wata cudanyar da ta shafi ayyukan soji ga yankin.

Jami’in ya ce Sin za ta ci gaba da daukar dukkanin matakan da suka wajaba gwargwadon sauyawar yanayi, za ta kuma kare moriyar mulkin kai da tsaron ta yadda ya kamata.     (Saminu)