logo

HAUSA

Yan wasan kasar Sin za su halarci dukkan rukunin wasanni shida na gasar nakasassu ta 2022

2022-02-21 11:01:01 CRI

Yan wasan kasar Sin za su halarci dukkan rukunin wasanni shida na gasar nakasassu ta 2022_fororder_0221-Paralympics-Ahmad

Yong Zhijun, mataimakin daraktan sashen wasannin nakasassu na kasar Sin ya bayyana a taron manema labarai cewa, ’yan wasan kasar Sin za su halarci dukkan rukunin wasanni shida na ajin gasar nakasassu na lokacin sanyi na Paralympic 2022.

Za a gudanar da wasannin motsa jiki na nakasassu na hunturu na 2022 a dukkan shiyyoyi uku na wasannin, da suka hada da tsakiyar Beijing, da gundumar Yanqing a Beijing, da kuma birnin Zhangjiakou na lardin Hebei, daga ranar 4 zuwa 13 ga watan Maris, inda za a fafata adadin wasanni 78 a nau’ikan wasannni shida.

A cewar Yong, ajin gasar wasannin nakasassu na kasar Sin na wasan kankara yana kara samun bunkasuwa cikin sauri a ’yan shekarun da suka gabata wanda kumshi karuwar mahalarta da kuma samun nasarori. Kasar Sin ta samu gagarumin bunkasar gasar nakasassu ta lokacin sanyi tun a shekarar 2016, yayin da adadin ya karu daga 50 zuwa kusan 1,000. A gasar nakasassu ta lokacin hunturu ta PyeongChang, tawagar ’yan wasan nakasassu ta lokacin sanyi ta kasar Sin ta yi nasarar lashe lambar zinare na farko a tarihi. (Ahmad)