logo

HAUSA

Ina dalilin da ya sa Beijing ta zama zakaran gwajin dafi wajen shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu?

2022-02-21 20:42:17 CRI

Ina dalilin da ya sa Beijing ta zama zakaran gwajin dafi wajen shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu?_fororder_11

A wajen bikin rufe gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta bana, wanda aka yi jiya Lahadi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta kasa da kasa wato IOC, Mista Thomas Bach ya gabatar da jawabi, inda a cewarsa, gasar Olympics ta bana, gasa ce da ba’a taba ganin irinta ba a tarihi.

Kwamitin IOC shi ma ya yi irin wannan tsokaci game da gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi, wadda aka gudanar a Beijing shekaru 14 da suka wuce. Tun daga shekara ta 2008 zuwa bana, kasar Sin ta shaidawa duk duniya cewa, ita kasa ce dake tsayawa haikan kan manufar gasar Olympics, tare da aiwatar da ita yadda ya kamata.

Ina dalilin da ya sa Beijing ta zama zakaran gwajin dafi wajen shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu?_fororder_22

Abu mafi muhimmanci a nan shi ne, ganin yadda cutar COVID-19 da sauran wasu kalubaloli ke ci gaba da addabar al’ummomin duniya, Beijing ta yi nasarar gudanar da gasar Olympics cikin lokaci, al’amarin da ya kara inganta hadin-gwiwa da zaman lafiya a duk fadin duniya. Bach ya kuma ce, hadin-gwiwa a wajen gasar Olympics, ta fi ‘yan a-ware karfi. Har ma shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta kasar Ukraine Sergey Nazarovich Bubka ya ce, sakon da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka yi a Beijing ta aikewa duniya shi ne, ‘yan Adam za su iya zama tsintsiya madaurinki daya, wajen samun galaba kan cutar COVID-19.  (Murtala Zhang)