logo

HAUSA

Yan majalisun Iran: Tilas ne “masu saba rantsuwa” na yammacin duniya su bada tabbaci kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya

2022-02-21 10:38:58 CRI

Yan majalisun Iran: Tilas ne “masu saba rantsuwa” na yammacin duniya su bada tabbaci kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya_fororder_0221-Iran-Ahmad

Mambobin majalisar dokokin Iran sun bayyana cewa, gwamnatin Iran ba za ta kulla wata yarjejeniyar nukiliya da kasashen yammacin duniya ba har sai sun ba ta tabbacin cewa ba za su yi watsi da yarjejeniyar ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarun kasar IRNA ya ba da rahoto.

Sanarwar wadda ’yan majalisar 250 suka rattaba hannu, sun gabatarwa shugaban kasar Ebrahim Raisi tare a karantawa yayin zaman majalisar dokokin kasar, inda suka bukaci shugaban kasar Iran da tawagar wakilan tattaunawar da su mayar da moriyar al’ummar kasa a gaban komai a yayin tattaunawar ta birnin Vienna, kana su guji shigar da kansu cikin duk wata yarjejejniya da kasashen yammacin duniya “masu saba rantsuwa” ba tare da sumun tabbaci ba.

Sanarwar ta ce, matsayar Iran game da tattaunawa kan batun dage takunkumi ya riga ya kai muhimmin mataki, kuma kasar tana maraba da duk wani matakin diflomasiyya wanda Raisi ya gamsu da shi da kuma tawagar mahalartar tattaunawar ta Vienna.

A cewar sanarwar, yau shekaru sama da takwas da suka gabata, kasashen Amurka, da Faransa, da Birtaniya, da kuma Jamus, sun tabbatar cewa, ba su cika ko da guda daga cikin alkawurransu ba, kuma za su yi amfani da dukkan damammakinsu wajen lahanta moriyar al’ummar kasar Iran duk kuwa da dokokin kasa da kasa. (Ahmad)