logo

HAUSA

Harshe na asali yana da daraja matuka

2022-02-21 21:45:57 CRI

Harshe na asali yana da daraja matuka_fororder_hausa-2

Yau rana ce ta harshe na asali, wadda hukumar UNESCO ta kebe don tunatar da al’ummun duniya muhimmancin kare yarensu na asali.

Dalilin da ya sa harshe na asali ke da muhimmanci, shi ne yana da amfani wajen bambanta mu da sauran al’ummomi. Saboda haka, harshenmu na asali tamkar lu’u-lu’u ne da aka gaje su daga magabantanmu. Sai dai wasu daga cikin “lu’u-lu’un” sun riga sun bace. Yau na karanta wani labari dake cewa: wata mace mai suna Cristina Calderon ta rasu a kwanakin baya, tana da shekaru 93 a duniya, da rasuwar ta kuma an rasa mutum ta karshe tsakanin dukkan mutanen duniya, wadda ta iya yaren Yamana, wani harshe na ‘yan kabilar Yagan a kasar Chile. Ko da yake ana ci gaba da samun wasu mutane fiye da goma, wadanda suke kiran kansu da ‘yan kabilar Yagan, amma tun tuni sun daina koyon harshen wannan kabila wato harshen Yamana, da magana da shi. Saboda haka, wannan yare shi ma ya mutu yanzu.

Bisa alkaluman da MDD ta samar, an ce a kalla kashi 43% cikin dukkan harsuna kimanin 6000 da ake samu a duniyarmu, suna bakin mutuwa. Cikin sauran harsuna, wasu fiye da dari daya ne kawai ke taka muhimmiyar rawa a fannonin aikin ilmantarwa, da mu’ammalar jama’a. Idan ana son kirga harsunan da ake iya buga su da na’urar kwamfuta, da rubuta bayanai da su a shafukan yanar gizo ta Internet, to, ba za su wuce dari daya ba.

Wasu dalilai da yawa sun sa harsuna na asali fadawa cikin mawuyacin hali: Misali, wasu al’adu na yaduwa a duniya, lamarin da ya sa ake kara yin amfani da yaren dake tare da al’adun, wanda ya kunshi fina-finai na Hollywood, da wakoki na Turanci masu farin jini, da makamantansu. Ban da wannan kuma, wayar salula ta zamani, da manhajar sadarwa sun sa muke kara fada wa juna magana, maimakon rubuta wasu sakonni, ta yadda mu kan manta da rubutaccen harshe. Haka zalika, kalmomi na harsunan waje, da maganganun da ba su yi daidai ba, sun cika shafukan Internet, wannan batu ya kara matsalar rashin yunkurin daidaita harshe, da koyar da shi ga dalibai, sun sa an shiga wani yanayi na fama da rikici a fannin yin amfani da yaren, abun da ke ba mutane wahala lokacin da suke son magana da juna, ta yadda sannu a hankali, ake fara yin amfani da harsunan ketare maimakon na asali.

Saboda haka, muna samun wakoki, da wasannin kwaikwayo, da sauran al’adun gargajiya, wadanda da akwai, amma yanzu babu, a wasu wurare daban daban. A wasu kasashe, idan wani mutum na son neman wani littafin da aka rubuta da yaren kasar na asali, game da tarihi na kasar, ba zai samu ba, illa dai littattafan da mutane na sauran kasashe suka rubuta kan tarihin kasar. Watakila akwai karairayi a cikin wadannan littattafai, amma mutum ba shi da sauran zabi. Kana wani abun da ya fi janyo damuwa shi ne: Yara suna magana da karin kalmomin harshen waje, da sauraron karin wakokin ketare, da kokarin kwaikwayon abubuwan da aka yi cikin bidiyo mai ban dariya na sauran kasashe, to, ko za su darajanta al’adun kabilar kansu? Shin suna kishin kasarsu?

Abu mafi bakanta rai shi ne, yaran ba sa sani ba sun rasa wani abu mai matukar daraja. Saboda ba za a san abubuwa masu ban sha’awa cikin wasu al’adu, idan ba a fahimci harshe mai alaka da al’adun ba. Misali, cikin harshen Hausa, akwai wani karin magana wato “Da kadan kadan matankadi ke shiga cikin gora”, maganar da ta kan iya sanya mutum tunanin ayarin matafiya: Wani matafiyi yana zaune yana hutawa a dab da wata rijiya, daga baya ya ga wani matankadi ya shiga cikin goransa. Ba a iya ganin kansa, sai dai wutsiyarsa dake bakin goran. Wannan abun ban sha’awa yana cikin wata gajeriyar jimla. Ban da wannan kuma, harshe na asali na iya karfafa zumunci da hadin gwiwa. Ba zan taba mantawa ba, lokacin da wani aboki na Bahaushe ya fada min “Ha!”, sai na bude baki kamar zan ce “Ah” amma ba tare da fitar da murya ba, abun da ya matukar burge shi, da sanya shi murna. Ya ce ya samu wani dan uwa a kasar Sin, saboda na iya Hausa, wato yarensa na asali.

Bari mu yi kokarin kare harshenmu na asali, kamar dai yadda ake kokarin kare lu’u-lu’un da ake gadonsu daga magabata. Don amfanin al’ummarmu da kasarmu, da kuma yaranmu. (Bello Wang)