logo

HAUSA

CMG ya taimakawa wajen gabatar da shirye-shirye game da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu cikin nasara

2022-02-21 10:55:31 CRI

CMG ya taimakawa wajen gabatar da shirye-shirye game da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu cikin nasara_fororder_0221-01

A wajen gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da aka gudanar a birnin Beijing a wannan karo, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya yi amfani da fasahohin zamani da tura kwararrun wakilai don gabatar da shirye-shiryen gasar da bikin bude gasar da na rufe gasar cikin nasara.

A gun gasar a wannan karo, CMG ya tura wakilai kimanin dubu uku don shiga aikin gabatar da shirye-shiryen gasar, wadanda suka cimma nasarar aikin gabatar da shirye-shiryen gasar ta hanyar fasahar 4K karo na farko a tarihi, da kuma samar da hotunan bidiyo da aka dauka a wajen bikin budewa da na rufewa gasar da kuma gasar wasan gudun kankara ta hanyar fasahar 8K. Kana na’urorin daukar bidiyo masu amfani da fasahar 4K da sauran na’urorin zamani da CMG ya kirkiro da kansa sun taimaka wajen gabatar da shirye-shiryen gasar cikin nasara. A gun gasar a wannan karo, kafofin telebijin 14 da kafofin rediyo 17 na CMG sun gabatar da shirye-shiryen gasar a dukkan fannoni.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya wato IOC Thomas Bach ya bayyana cewa,“CMG ya gabatar da shirye-shiryen gasar cikin nasara, kuma ya samar da babbar gudummawa ga kwamitin IOC wajen taimakawa kamfanin gidan rediyon IOC wato OBS, kana ya samu nasara wajen gabatar da shirye-shirye ga duk duniya.” (Zainab)