logo

HAUSA

Katafaren madatsar ruwan Habasha ya fara samar da hasken lantarki

2022-02-21 14:35:39 CMG

Katafaren madatsar ruwan Habasha ya fara samar da hasken lantarki_fororder_0221-Habasha-Ahmad(1)

Gwamnatin kasar Habasha ta sanar a ranar Lahadi cewa, dam din da ta gina, wanda aka fi sani da (GERD), ya fara samar da karfin wutar lantarki ta ruwa.

Aikin samar da lantarkin na farko na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen dake makwabtaka da Habashan wato Masar da Sudan ke nuna damuwa game da fargabar cewa aikin madatsar ruwan zai iya yin barazana wajen rage adadin ruwan da suke bukata don amfanin kasashensu.

Sai dai kuma, gwamnatin Habashan tana ikirarin cewa, dam din yana da matukar alfanu wajen bunkasa lantarki da kuma cigaba, kana ba zai haifar da illa ba ga sauran kasashen dake bakin kogin Nilu.(Ahmad)

Ahmad