Yahaya Muhammad mai nazarin shirye-shiryen sashin Hausa na CRI
2022-02-21 21:02:17 CRI
Yahaya Muhammad Makarfi, wani dan asalin jihar Kadunan Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a kan harshen Hausa a jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang kwanan nan, Yahaya Muhammad Makarfi ya bayyana tarihinsa na sauraro, gami da nazarin shirye-shiryen sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin wato CRI HAUSA, da dalilin da ya sa yake matukar sha’awar wadannan shirye-shirye.
A cewarsa, shirye-shiryen sashin Hausa na rediyon Sin suna da bambance-bambance da yawa, idan aka kwatanta da na kafafen yada labarai na kasashen yamma. (Murtala Zhang)