logo

HAUSA

Sin tana fatan kungiyar EU za ta gyara ra’ayin kuskure da ta nunawa Sin

2022-02-21 11:22:46 CRI

Kakakin tawagar jakadun Sin dake kungiyar EU ya yi bayani game da ra’ayin kungiyar EU da aka gwada a gun taron kiyaye tsaro na Munich a jiya, inda ya bayyana cewa, kasashen yammacin duniya na fuskantar matsaloli, ya kamata su nemi dalilin da ya sa hakan daga kansu. A cikin dukkan manyan matsalolin da suka ko suke faruwa a sassa daban daban na duniya, ko babu kasashen yammacin duniya da suka ko suke tsoma baki ko sa hannu, har ma suka tayar da hankali kai tsaye?

Kakakin ya yi nuni da cewa, ya kamata mu magance bin ra’ayin yakin cacar baka wajen tsaron kai a tsakanin kasashe daban daban, kuma kar a bi ra’ayin yakin cacar baka a tunanin filsofiya. Wannan ra’ayi ba zai samar da gudummawa ga kokarin yin mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin al’adu daban daban ba.

Kakakin ya jaddada cewa, kamar yadda memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a gun taron kiyaye tsaro na Munich a jiya cewa, duniya tana fuskantar hadarin nuna kiyayya da juna, ya kamata kasa da kasa su yi kokari tare, bai kamata a nuna kiyayya ga juna ba, ta hakan za a warware matsalolin dake kasancewa a duniya a halin yanzu, da samun kyakkyawar makoma. Sin da Turai su ne manyan bangarori biyu a duniya, tabbas suna da karfi wajen kiyaye zaman lafiya a duniya. Sin tana fatan bangaren Turai zai gyara ra’ayin kuskure da yake nunawa Sin, da yin hadin gwiwa tare da bangaren kasar Sin don kokarin gina “wata kyakkyawar duniya” cikin hadin gwiwa. (Zainab)