logo

HAUSA

Shugaban IOC ya bayyana rufe gasar Olympic ta hunturu ta Beijing

2022-02-20 22:11:34 CRI

Shugaban IOC ya bayyana rufe gasar Olympic ta hunturu ta Beijing_fororder_b90e7bec54e736d11153c4f347efa5cbd76269d6

Shugaban kwamitin wasannin Olympic ta kasa da kasa IOC, Thomas Bach, ya bayyana rufe gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 a yau Lahadi.

A jawabin da ya gabatar a bikin rufe gasar, Bach ya bayyana gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing da cewa “ta musamman ne."

A gun bikin rufe gasar, an kuma damka tutar Olympic ga magajin garin Milan da na Cortina d'Ampezzo, biranen da zasu karbi bakuncin gasar Olympic ta lokacin hunturu ta shekarar 2026.(Ahmad)