logo

HAUSA

Afirka ta nuna damuwa ko Turai za ta iya cika alkawurran da ta dauka a wajen taron kolin Turai da Afirka

2022-02-20 17:27:57 CRI

Afirka ta nuna damuwa ko Turai za ta iya cika alkawurran da ta dauka a wajen taron kolin Turai da Afirka_fororder_1128395738_16452720625661n

A ranar 18 ga wata, aka kammala taron koli tsakanin kungiyar tarayyar Turai EU da kungiyar tarayyar Afirka wato AU a birnin Brussels na kasar Belgium, inda aka cimma wasu nasarori a bangarorin da suka shafi sake tsugunar da al’umma, da kiwon lafiya, ciki har da wani shirin zuba jari ga kasashen Afirka da EU ta sanar, wanda ke kunshe da kudin EURO biliyan 150.

Masanin dangantakar kasa da kasa daga kasar Kenya, Cavins Adhill ya yi tsokaci kan nasarorin taron kolin, inda a cewarsa, duba da yadda nahiyar Afirka ke matukar bukatar zuba jari a fannin kiwon lafiya, shirin na EU yana da babbar ma’ana. Amma kamar yadda malam Bahaushe kan ce, kyan alkawari cikawa. Har yanzu, ba’a tabbatar wadanne fannoni wannan shirin zai goya musu baya, kuma wadanne kasashe ne zasu ci gajiyar shirin ba, da lokacin kammala shi, dukka ba’a sani ba.

Mista Adhill ya kara da cewa, al’ummar Afirka na son samun ci gaba, amma ba su bukatar zance fatar baki kawai wanda ke hade da barazana ko wasu sharudda. Idan mun dubi yadda aka cika alkawurran da EU ta dauka a wajen tarukkan kolin na baya, muna iya ganin cewa, babu wani abun da zai sa kasashen Afirka su sake amincewa, EU ta riga ta kafa wani sabon tsarin raya dangantaka tare da Afirka, wanda ke da adalci da samun moriyar juna da samar da ci gaba mai dorewa. (Murtala Zhang)