logo

HAUSA

Mutane 24 sun kubuta daga hannun masu garkuwa a arewa maso yammacin Najeriya

2022-02-20 16:30:46 CRI

Hukumar ‘yan sandan Najeriya a jahar Zamfara, dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya sun yi nasarar kubutar da mutane 24 daga hannun masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jahar Zamfaran ya fadawa taron ‘yan jaridu a Gusau, babban birnin jahar cewa, wadanda aka kubutar din sun hada har da wani jariri dan watanni bakwai da haihuwa, kuma an yi nasarar kubutar da su ne bayan musayar wutar da aka yi tsakanin jami’an tsaron da ‘yan fashin dajin a ranar Juma’a.

Shehu yace, rundunar ‘yan sandan ta samu kiran waya a ranar Juma’a, inda aka sanar da su cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun afkawa kauyen Gurgurawa sun yi garkuwa da wasu mazauna yankin da dama.(Ahmad)