logo

HAUSA

Putin: Amurka bata da niyyar kare muhimman bukatun tsaron Rasha

2022-02-19 16:22:47 CMG

Amurka bata da niyyar kare muhimman bukatun tsaron Rasha_fororder_0219-Rasha-Fa'iza

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa, har yanzu, Amurka da sauran kasashen kungiyar tsaro ta NATO, ba su da niyyar kare muhimman bukatun tsaron kasarsa yadda ya kamata.

Vladimir Putin ya bayyana haka ne, bayan ganawarsa da takwaransa na Belarus, Alexander Lukashenko.

Ya kara da cewa, ya yi wa takwaran na sa a Belarus bayani kan tattaunawarsa na baya-bayan nan da kasashen yamma, game da samun tabbacin tsaro dake da nisan zango da kuma karfin doka ga Rasha, daga wajen Amurka da kungiyar tsaro ta NATO.

Har ila yau, ya ce sun tattauna game da yadda al'amura ke gudana dangane da bukatun Rasha ga kasashen yamma, wadanda suka hada da kungiyar NATO ta yi watsi da shirinta na fadada kawancenta zuwa yankin gabashi, ta kuma yi alkawarin ba zata girke makaman yaki a kusa da iyakokin Rasha ba, kana ta koma ga tsare-tsarenta na ayyukan soji da na kayayyakin yaki a kasashen Turai, kamar yadda suke a shekarar 1997, a lokacin da ita da Rashar suka rattaba hannu kan yarjejeniya. Yana mai cewa, ya riga ya bayyana cewa, Amurka da sauran mambobin kungiyar ba su da niyyar kare wadannan muhimman bukatu 3 yadda ya kamata.

Haka kuma, shugaban na Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma sun shirya wasu sabbin dabaru game da tsaron Turai, da makamai masu linzami masu cin gajere da matsakaicin zango da tsare gaskiya a ayyukan soji, a matsayin wasu batutuwa da Rasha ke son tattaunawa kansu. (Fa'iza Mustapha)

Fa'iza