logo

HAUSA

An saki Jami'in MDD na karshe dake tsare a Habasha

2022-02-19 16:09:02 CMG

An saki Jami'in MDD na karshe dake tsare a Habasha_fororder_0219-Habasha-Fa'iza

MDD ta bayyana a jiya cewa, an saki jami'inta na karshe dake tsare a hannun hukumomin kasar Habasha.

Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na MDD ne ya bayyana hakan, inda ya ce, wannan batu ne da Amina Mohammed, mataimakiyar sakatare janar din ta tattauna kai da shugabancin kasar Habasha yayin ziyararta ta baya-bayan nan. Amina Mohammed ta yi ziyarar yini 5 a Habasha, cikin makon da ya gabata.

Sai dai, Stephane Dujjaric bai yi wani karin bayani kan jami'in ba, in banda cewa da ya yi, dan kasar ta Habasha ne.

Da aka tambaye shi ko jami'in da sauran jami’an majalisar biyu da aka saki kwanaki biyu kafin jiyan 'yan yankin Tigray ne, Dujarric ya ce MDD ba ta la'akari da kabilar jami'anta. Yana mai cewa, a wajensu, 'yan kasar Habasha ne dake yi wa majalisar aiki.

Ya kara da cewa, ana ci gaba da fuskantar kalubale wajen ayyukan jin kai a kokarin taimakawa mutanen da rikici ya shafa a arewacin Habasha. (Fa'iza Mustapha)

Fa'iza