logo

HAUSA

Mutane akalla 10 sun mutu sanadiyyar harin kunar bakin wake a Somalia

2022-02-19 20:17:10 CRI

‘Yan sanda da wasu ganau, sun shaida cewa, mutane akalla 10 sun mutu yayin da wasu 15 suka jikkata sanadiyyar wani harin kunar bakin wake da aka kai yau Asabar, garin Beledweyne na yankin tsakiyar Somalia.(Fa’iza)