logo

HAUSA

Dalibin Kongo DR ya sadaukar da zane ga wasannin Olympic na Beijing 2022

2022-02-18 10:45:05 CRI

Dalibin Kongo DR ya sadaukar da zane ga wasannin Olympic na Beijing 2022_fororder_220218-Ahmad2-Congo

Wani dalibin kwalejin fasaha a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, ya sadaukar da zanen da ya yi ga gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 a ofishin jakadancin kasar Sin dake Kinshasa, babban birnin Kongo DRC.

A cewar dalibin Bahati Kosi, zanen, wanda ya kunshi bangarori daban daban na gasar ta lokacin hunturu, ya yi hakan ne da nufin nuna jinjina bisa ga namijin kokarin da kasar Sin ta yi wajen nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 a wannan mawuyacin halin da duniya ke ciki na fama da annobar COVID-19.

Kosi ya ce, zane wata kyakkyawar hanya ce da al’ummar Kongo ke bayyana fatan alherinsu, musamman matasan kasar Kongo, zuwa ga aminan kasashe kamar kasar Sin, wacce ta sha taimakawa kasar Kongo DRC a fannoni daban daban, kamar bangaren ilmi.

Da yake karbar zanen, Zhu Jing, jakadan kasar Sin a DRC, ya yi maraba da aikin fasahar zanen wanda yake alamta ruhin gasar Olympic da kuma kyakkyawar dangantakar dake tsakanin al’ummun kasashen biyu.

Zhu ya ce, “yayin da a bana kasashenmu biyu ke murnar cika shekaru 50 da kulla muhimmiyar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, muna matukar farin ciki da wannan zane, kuma kyauta mai daraja wacce ke alamta burinmu na bai daya na daga matsayin alakarmu da kuma ci gaba da kasancewa tare don samun makoma mai kyau." (Ahmad Fagam)