logo

HAUSA

Xi Jinping ya ake da sakon jaje ga shugaban Brazil

2022-02-18 19:21:38 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa takwaransa na Brazil Jair Bolsonaro da sakon jaje, bisa mamakon ruwan sama da ya haifar da hasarar rayuka a kasar sa.

Ya zuwa jiya Alhamis, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe kwanaki ana yi, ya haddasa ambaliya, da zaftarewar kasa a birnin Petropolis na kasar, lamarin da ya sabbaba rasuwar a kalla mutane 117, baya ga wasu karin mutanen 116 da suka bace.  (Saminu)