logo

HAUSA

Sin: Bai dace a yi amfani da barazanar yaki a matsayin hanyar samun galaba game da rikicin Ukraine ba

2022-02-18 19:54:10 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce bai dace a yi amfani da barazanar yaki, a matsayin hanyar samun galaba game da rikicin Ukraine ba, idan har ana son warware takaddamar da ake yi ta hanyar siyasa.

Wang Wenbin, ya bayyana hakan ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, inda ya yi tsokaci kan tambayar da aka yi masa, game da kalaman sakataren wajen Amurka Antony Blinken na baya bayan nan, inda Mr. Blinken din ya zargi Rasha kan rikicin ta da Ukraine.  (Saminu)