logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin Nijar

2022-02-18 12:34:39 CRI

Jakadan Sin a Nijar ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin Nijar_fororder_微信图片_20220218112052

Jiya 17 ga wata, Jakadan kasar Sin da ke Jamhuriyar Nijar Jiang Feng, ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin Nijar Salifou Modi, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da hadin kansu ta fuskar tsaron sojoji.

Jakada Jiang ya bayyana cewa, hadin kan Sin da Nijar ta fuskar aikin soja wani muhimmin bangare ne na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A kwanakin baya, Shugaba Xi Jinping na Sin ya sanar da gudanar da manyan ayyuka tara tare da kasashen Afirka a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin hadin kan Sin da Afirka na FOCAC, ciki har da babban aikin tsaro da zaman lafiya. Sin na son kokari tare da Nijar don inganta hadin kan sojojin kasashen biyu, ta yadda za a ciyar da dangantakar da ke tsakanin sojojin biyu gaba.

A nasa bangaren, Salifou Modi ya ce, akwai dankon zumunci a tsakanin Nijar da Sin, duk da kasancewar Nijar na fuskantar kalubale a fannin hare-haren ta’addanci da dai sauransu, amma Sin na ci gaba da mara wa Nijar din baya wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. An samu kyawawan sakamako a tsakanin kasashen biyu a fannin tsaron sojoji, kasarsa na yi wa Sin matukar godiya bisa horar da jami’an sojojinta da samar da taimako. (Kande Gao)