logo

HAUSA

Sudan ta kudu ta yaba ci gaban da aka samu a aikin talabijin da kasar Sin ke gudanarwa

2022-02-18 11:43:17 CRI

Sudan ta kudu ta yaba ci gaban da aka samu a aikin talabijin da kasar Sin ke gudanarwa_fororder_220218-Ahmad3-South Sudan

Wani jami’in kasar Sudan ta kudu ya yaba yadda ayyukan da kamfanonin gine-gine biyu na kasar Sin ke gudanarwa suke gudana ciki sauri a babban gidan radiyo da talabijin na kasar.

Ramadan Kamil Abulangi, daraktan sashen injiniya na babban gidan radiyon kasar Sudan ta kudu (SSBC), ya ce, aikin wanda aka fara gudanawa a shekarar 2019 zai kawo gagarumin sauyi ga ayyukan yada labarai na gidan radiyo da talabijin na kasar idan aikin ya kammala a watan Agusta.

Kamfanonin China Dalian International Economic and Technological Cooperation Group Co. Ltd da Beijing Yutian Suocheng Technology Co. Ltd ke gudanar da aikin bisa hadin gwiwa.

Kamil ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wannan aiki ne mafi muhimmanci ga Sudan ta kudu saboda za a samar da na’urar yada shirye-shirye mai tsawon mita 120, kuma za a samar da yanayin sadarwa wanda zai hada fadar shugaban kasar yayin da ake watsa shiri na kai tsaye, sannan za a samar da wani yanayin sadarwar wanda zai kewaye birnin Juba don watsa dukkan shirye shiryen da ake gabatarwa kai tsaye. (Ahmad)