logo

HAUSA

An cimma manyan nasarori a fannin gina Sin mai kayatarwa da gasar Olympic maras gurbata muhalli

2022-02-18 19:34:12 CRI

An cimma manyan nasarori a fannin gina Sin mai kayatarwa da gasar Olympic maras gurbata muhalli_fororder_muhalli

A yau Juma’a ne, cibiyar watsa labarai game da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing, ta gudanar da taron manema labarai, inda ta gabatar da jerin matakai, da sakamako da aka cimma, wajen gina Sin mai ban sha’awa, da gudanar da gasar Olympics ta 2022 ba tare da gurbata muhalli ba.

Rahotanni daga taron sun bayyana cewa, an cimma manyan nasarori a fannin kare muhalli, yayin gasar ta Olympics daidai da yadda ake bukata, kana an yi amfani da kaso 100%, na makamashin lantarki maras gurbata muhalli a yayin gasar.

Cikin shekaru 5 da suka gabata, ingancin yanayin muhallin halittu na Sin, ya ci gaba da kyautatuwa. Bugu da kari, Sin ta zamo ta daya a duniya, a fannin kakkafa na’urorin samar da lantarki ta hasken rana da iska, da ma yawan sayar da ababen hawa masu amfani da makamashi da ake sabuntawa. (Saminu)