logo

HAUSA

Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance

2022-02-17 20:55:42 CRI

Sharhi daga Lubabatu Lei

Jama’a, shin me za ku ce game da ma’anar gudanar da gasar wasanni ta Olympics?

Yin takara don neman cin lambobi ne? Babu shakka, wannan wani bangare ne na gasar, amma ba shi ke nan ba.

‘Yan kwanaki suka rage za a kawo karshen gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ke gudana a nan birnin Beijing. A cikin kwanakin da suka gabata, yadda ‘yan wasan daga kasa da kasa suka kokarta matuka, don cimma karin nasarori a yayin gasar ya burge mu ainun, sai dai baya ga haka, yadda ‘yan wasan suke cudanya da juna bayan gasar ya fi sosa mana rai.

Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance_fororder_微信图片_20220217205317

Kwanan baya, ’yar wasan kasar Sin Xu Mengtao ta zama zakara da maki 108.61, a wasan tseren kankara da ake sarrafa jiki a iska na Freestyle Skiing na gasar. Nan da nan, ‘yar wasan kasar Amurka Ashley Caldwell ta rungume ta, har hawaye ya zubo mata sabo da murna. Ta ce, yadda Xu Mengtao ta yi iyakacin kokari a gasar ta burge ta, kuma ya sa tana girmama ta. Ta yi murna da yadda Xu mengtao ta cimma mafarkinta a kasarta ta mahaifa.

Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance_fororder_微信图片_20220217205327

A gasar wasan Curling, ‘yan wasan kasar Amurka Vicky Persinger and Chris Plys, sun yi nasara a kan ‘yan wasan kasar Sin Ling Zhi da Fan Suyuan. Bayan da gasar ta kare, ‘yan wasan kasar Sin sun mika wa abokan takararsu ‘yan tsarabobi, wato bajoji masu siffar Bing Dwen Dwen, ‘yar tsanar gasar a wannan karo, matakin da ya burge ‘yan wasan Amurka, har suka bayyana cewa “so cool” wato dai hakan ya burge su, kuma sun saka hotonsu a shafinsu na sada zumunta. Kafar NHK ta kasar Japan ma ta ce, gasar ta kusantar da ‘yan wasan kasashen biyu da juna. 

Yadda ya kamata gasar Olympics ta kasance_fororder_微信图片_20220217205333

Bayan gasar tseren kankara ta gajeren zango, ta yada kanin wani ta mita 3000 ajin mata, ‘yan wasan kungiyoyin kasashen Netherlands, da Koriya ta Kudu, da kasar Sin, da suka ci lambobin zinari da azurfa da tagulla, sun hadu sun dauki kansu hotuna na selfie, cikin murna da farin ciki……

A gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, an sha ganin irin zumuntar da ‘yan wasan suka kulla. Lallai, ‘yan wasan dake fafatawa a gasar abokan takara ne, sai dai kuma sun kasance aminan juna da ke neman karin ci gaban dan Adam kafada da kafada.

Yadda aka gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing bisa lokacin da aka tsaida, ya samar da wata gadar fahimtar juna a tsakanin ‘yan wasan kasashe daban daban, tare da samar da damar karfafa hadin kan ‘yan Adam, kuma ‘yan wasan gasar sun shaida mana ruhin gasar, wato “Faster Higher Stronger da ma Together”. Wato Karin sauri, dagawa, karfi da tafiya tare”.