logo

HAUSA

Kwararren kasar Ghana ya ce alfanun AfCFTA ga kamfanonin sarrafa kayayyaki gagarumi ne

2022-02-17 11:13:26 CRI

Kwararren kasar Ghana ya ce alfanun AfCFTA ga kamfanonin sarrafa kayayyaki gagarumi ne_fororder_A03-AfCFTA

Wani kwararren masanin harkokin kasuwancin kasar Ghana ya yi hasashen cewa alfanun da za a samu daga yarjejeniyar ciniki maras shinge ta nahiyar Afrika wato (AfCFTA) za ta haifar da bunkasar kamfanonin sarrafa kayayyaki na nahiyar tun bayan fara aiki da yarjejeniyar yau shekara guda da ta gabata.

Jonas Atangdui, daraktan sashen nazarin al’amurran tattalin arziki a cibiyar Kwame Nkrumah Ideological Institute, wato cibiyar tsara manufofin ci gaba ta kasar, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, AfCFTA za ta samar da guraben ayyuka, da kudaden shiga da na haraji ga gwamnatoci, kana za ta rage yawan kudaden da gwamnatocin Afrika ke biya wajen shigo da kayayyaki ta hanyar kafa masana’antun sarrafa kayayyaki na cikin gidan nahiyar.

Taron ministocin kasuwanci na kungiyar tarayyar Afrika AU wanda aka gudanar a ranar 29 ga watan Janairu ya sanar da cewa, an kammala tattaunawa tare da amincewa da dokoki na asali wanda zai shafi kashi 87.7 bisa 100 na kayayyakin da ake kasuwancinsu a tsakanin mambobin kasashen AU. Wadannan dokoki sun kunshi hanyoyin da ake amfani da kayayyakin da aka samar a kasa, ta hakan ne za a duba irin harajin da ya cancanta da kuma kariyar da kayayyakin ke da ita karkashin yarjejeniyar kasuwancin. (Ahmad Fagam)