Karbuwar da gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta samu ya isar da babban sako!
2022-02-17 20:01:13 CRI
Alkaluma sun nuna cewa, kawo yanzu, adadin wadanda suka kalli gasar Olympics ta lokacin sanyi birnin Beijing dake gudana yanzu haka, ya kai matsayin koli a tarihin gasar, inda a jiya Laraba, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta kasa da kasa IOC, da kwamitin shirya gasar na Beijing, suka haifar da gagarumar muhawara tsakanin masu fashin baki a sassan duniya.
Kafin hakan, tuni shirye shiryen gasar ta Olympic ta lokacin sanyi ta 2022 dake gudana, suka samu masu kallo sama da biliyan 2 a fadin duniya, kana labarai da sharhi game da gasar suka karade sassan shafukan sada zumunta.
Ko shakka babu, karbuwar da gasar ta Olympics ta birnin Beijing ta samu, ya isar da babban sako! Inda baya ga kawar da hasashen wasu kafofin yamma cewa gasar ba za ta yi armashi ba, a hannu guda, gasar ta nuna matukar kauna, da jin dadi, da kawance da wasannin kankara da na dusar kankara suka haifar, kana gasar ta hallara al’ummun kasashen duniya daban daban. A yayin wannan gasa, hadin gwiwa, da karfin hali da kwazo, ya karfafa imanin kasashen duniya. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)